Akwai Bukatar Shugabanni Su Kara Tashi Tsaye Domin Kawo Karshen Matsalar Tsaro-----Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga musulmai da su fita su karbi katin zabe domin hakan zai sa su zabi wanda suke so, rashin hakan zai sa a zabar musu wanda ba shi suke bukata ba.
“Ina kira ga muslmai na Sakkwato da sauran jijhohin Nijeriya, yanzu ana karbar katin zabe in ba ka da shi ba ka zabe, ka ga ba za ka zabi wanda ka ke so ba, muna kira da murya mai karfi ga musulmai a fita a karbi katin zabe komi wahalar da ke ciki domin ranar zabe a zabi wanda yakamata da zai taimaki addini da jama’a a Nijeriya baki daya”.
Sarkin musulmi ya yi wannan jawabi ne a sakonsa na barka da sallah a fadarsa ya ce kowa ya fito kwansu da kwarkwata a yanki katin zabe, “in ka karbi katin zabe kar ka baiwa dan siyasa ya ajiye maka, ka rike shi hannu biyu,” a cewar Sa’ad Abubakar.
Ya bayyana matsalaolin da Sakkwato ke fama da su na rashin ruwan sha da abinci, gwamnati na kokarin shawo kan matsalolin a jiha da kasa baki daya.
Sarkin Musulmi ya ce akwai bukatar a yi wa kasa da shugabanni addu’a nan da lokacin kadan za a shiga siyasa “fatanmu a yi lafiya a kare lafiya Allah ya ba mu shugabanni da za su tausaya mana da addininmu, su sanya jiha da kasa cigaba, gwargwado ana kokari amma akwai matsalar rashin tsaro a ko’ina cikin kasarmu, akwai bukatar shugabanni su kara tashi tsaye domin kawo karshen matsalar tsaro, abin da ke hana manoma tafiya gona yana dumuwarmu domin duk al’ummar da ba ta da abinci tana cikin matsala, yakamata gwamnati ta kawo karshen wannan matsalar,” a cewarsa.
Ya ce yana aiki tare da gwamnan Sakkwato bisa gaskiya da amana domin ciyar da jiha gaba yana fatan hakan ya dore.
managarciya