Akpabio ya gano kura-kurai a sabon taken Nijeriya
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gano kurakurai a cikin layi na uku da na biyar da na 18 a gyararren taken Nijeriya da hukumar wayar da kan jama’a, NOA, ta fitar.
Akpabio ya ce ya lura da kura-kurai a yayin zaman majalisar a jiya Talata, ya kuma umarci hukumar NOA da ta gaggauta gyara kura-kuran.
A ranar Larabar da ta gabata ne Darakta-Janar na NOA, Lanre Issa-Onilu, ya kaddamar da tataccen taken na kasa a Abuja.
Mista Issa-Onilu, a yayin kaddamar da bikin, ya bukaci ‘yan Najeriya da su kula da kalmomin da ke cikin layi na uku da biyar na taken da hukumar ta fitar.
"Muna jan hankalin ƴan Najeriya su maida hankali kan layi uku na farko, wanda ke cewa: 'Ko da yake kabilanci da harshe na iya bambanta'.
managarciya