Aisha Buhari ta yi wa Shaikh Isah Ali  Pantami Wa'azi

Aisha Buhari ta daura bidiyon Pantami in da yake kuka ta ce a cire tsoro a yi abin da ya dace.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a ranar Lahadi ta daura Bidiyo in da Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani Shaikh Isah Ali Pantami yake kuka a dayan wa'azin da ya yi kan jawo hankalin mutane su ji tsoron Allah da abin da ya tanadar ga masu jin tsoronsa.

Shaikh Pantami da Alaramansa sun fashe da kuka bayan karanta wasu ayoyin Kur'ani kan jin tsoron Allah da abin da Allah ya tanadar wa masu tsoronsa na Aljannarsa da rahamarsa, a yayin da yake yi wa mahalarta wa'azinsa bayani.

Aisha ta daura bidiyon ne a turakara ta Instagram sai ta yi wannan bayanin: "A chire tsoro a yi abin da ya dace." 

Abin da kawai ta rubuta ba ta yi wani karin bayani ba, abin da ke nuni da cewa ita ma wa'azi ne ta yi masa.

A bidiyon da baya da yawa  Alarama ya karanta aya ta 63 a cikin suratul Maryam a locin da Pantami yake fassarawa kuka ya kwace masa bayan Alarama na yin kukan sai ya roki Allah ya sanya shi cikin bayinsa salihai ya ce "Allah ka sani cikin su, Allah ka sani cikin su".