Aisha Buhari Ta Ba Ma'aikatanta Hutu Su Tafi Sai Ta Neme Su

Aisha Buhari Ta Ba Ma'aikatanta Hutu Su Tafi Sai Ta Neme Su

Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta baiwa ma'aikatanta hutun karshen shekara su tafi har sai ta neme su.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Dokta Muhammad Kamal, babban hadimi na musamman ga uwargidan shugaban kasar kan harkokin kiwon lafiya.

Dakta ya ce duk wani da zai kama za a nemi su gabatar a wajen ofis ba sai sun zo ba.
Sanarwar ta kuma ce uwargidan shugaban kasar tana godiya kan jajircewarsu tare da taya dukkan ma’aikatan murna a yayin da shagugulan bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara suka karato.
Wannan matakin ya zo bayan jita-jitar da ake yadawa a kafofin sada zumunta wai uwargidan na dauke da juna biyu.

Mai magana da yawunta ya karyata zancen ya ce magana ce maras tushe balle makama.