Aikin soja: Jihar Kebbi ta samu mukaman Janaral  7 a lokaci guda

Aikin soja: Jihar Kebbi ta samu mukaman Janaral  7 a lokaci guda

Gwamnatin  jihar Kebbi karkashin jagorancin Dakta Nasir Idris ta taya murna ga 'yan asalin jihar su Bakwai da suka samu karin girma zuwa matakin Janaral a aikin sojan Nijeriya.

 
Karin Girman nasu ya zo ne bayan da hukumar sojojin kasa ta sanar, in da ya kunshi sojan sama da ruwa dana kasa.
 
Kwamishinan yada labarai a jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed BK amadadin gwamnatin Kebbi ne ya fitar da bayanin ya ce Gwamna Nasir ya yi farinciki da labarin karin girman da mutanen jiharsa 7 suka samu.
 
A cewarsa mutanen da suka samu karin girman sun hada da Mejo Janarar WB Idris da M Adamu dukansu daga karamar hukumar  Ngaski, sai  Major General GS Mohammed a karamar hukumar Bagudo da  Major General GA Suru daga karamar hukumar Suru.
 
Sai a gefen sojojin ruwa akwai  Navy Commodore SM Tasi’u daga karamar hukumar Yauri;  da Air Vice Marshal ZA Usman a karamar hukumar Birnin Kebbi  da  Air Commodore SM Chindo ya fito daga karamar hukumar Argungu.
 
Kwamishina Alhaji Yakubu a kalamansa ya nuna Gwamna da mutanen jihar Kebbi gaba daya suna farinciki da wannan cigaba da aka samu ga mutanen da suka jajirce a wurin ciyar da kasa gaba a gefen aikin soja.
 
 
Alhaji Yakubu Ahmed ya ce Gwamna yana alfahari da su musamman yanda suka yi tsaye don ganin an shawo kan matsalar tsaron da ke addabar Nijeriya domin ganin abin ya zama tarihi.
 
Ya gode masu yanda suka yi tsayin daka a wurin aiki cikin kishin kasa hakan ne ya sa suka kai in da ake bukata. Akwai bukatar mutane su cigaba da yin da addu'a ga jami'an tsaron kasa domin ganin an kawar da 'yan bindiga da sauran bata garin da suka addabi al'ummar Nijeriya.
 
 
Gwamnan ya yi kira ga wadanda suka samu karin girman da su kara kaimi don tabbatar da cigaba da bin doka da oda a kasar Nijeriya.
 
Jihar Kebbi tana cikin jihohin Nijeriya dake da yawan mutane a harkar soja a yankin Sakkwato ita ce kan gaba a yawan sojoji manya da kanana.
 
Sake samun karin girma da wadannan sojoji suka yi zai sa jihar ta ci gaba da rike kambin da take da shi tsakanin jihar Sakkwato da Zamfara a harkar soja.