Aikin Hajji: Gwamnatin Katsina za ta biya kuɗin Hadaya Ga maniyata

Aikin Hajji: Gwamnatin Katsina za ta biya kuɗin Hadaya Ga maniyata
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD. yayi kira ga Kwamitin daya kafa wanda zai gudanar da ayyukan aikin Hajji na shekarar 2024 dasu jajir ce wajen gudanar da aikin su.
Gwamnan yayi wannan kira ne a lokacin da yake ƙaddamar da Kwamitin a Fadar Gwamantin Jihar.
Yakuma faɗa cewa akwai buƙatar Mambobin Kwamitin da su kasance masu aiki kafaɗa da kafaɗa da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jiha domin samun nasarar aikin baki ɗaya.
Gwamna Raɗɗa ya sanar cewa kasancewar wannan shine aikin Hajji da Gwamnati maici zata fara gudanarwa, akwai buƙatar Mambobin Kwamitin da dukkan masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye wajen ganin nasarar aikin.
Gwamna Raɗɗa ya kuma buƙaci Mambobin Kwamitin da su samar da cikakkun bayanai da za su sa a inganta aikin Hajji mai zuwa bayan kammala aikin su.
Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa PhD. ya kuma yi masu fatan alkairi da samun nasarar gudanar da aikin su.
Gwamnan ya kuma yaba ma Mahajjatan Jihar Katsina akan ƙoƙarin su na cika dukkanin kuɗaɗen da Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta ƙayyade, sai ya bada tabbacin Gwamnatin Jiha wajen samar da jin daɗi da walwalar Mahajjatan tare da yi masu Alkawarin biyama kowane Alhaji kudin hadaya wanda suka kama riyale 720 kwatankwacin Naira 280,000.
Daga ƙarshe Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da Shugaba da Mambobin Kwamitin da suka hada da tsohon mataimakin gwamna, Alh.Tukur Ahmed Jiƙamshi shi ne zai jagoranci tawagar.