Home Siyasa ADC ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya sake nazarin salon...

ADC ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya sake nazarin salon mulkinsa yayin cika shekaru 74 da haihuwa

8
0

Jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, da ya yi nazari kan salon jagorancinsa yayin da yake bikin cika shekaru 74 a duniya.

A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce ‘yan Nijeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da matsalar tsaro a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa farashin mai ya ƙaru sosai tare da tsadar rayuwa.

Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa kan matsalar tsaro, tana mai cewa Nijeriya ta koma matsayi na huɗu a jerin ƙasashen da ke fama da ta’addanci, tare da asarar rayuka da tarwatsa al’umma.

Sai dai ADC ta ce ranar haihuwa lokaci ne na yin nazari, inda ta yi addu’ar Allah ya ba shugaban ƙasa lafiya da kyakkyawar fahimta domin ɗaukar matakan da za su inganta rayuwar ‘yan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here