Home Siyasa ADC ta fallasa shirin APC na zanga zangar tayar da hankali a...

ADC ta fallasa shirin APC na zanga zangar tayar da hankali a Abuja

2
0

ADC ta fallasa shirin APC na zanga zangar tayar da hankali a Abuja da nufin kawo rikici a jam’iyyar don kawai Sen Rabi’u kwankwaso Ya shiga jam’iyyar ADC.

Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin APC da shirya wani sabon salo na rikita siyasa domin kawo cikas ga jam’iyyar, bayan sauyin sheƙa da H.E. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zuwa ADC.

A cewar jam’iyyar, bayan da suka kasa samun nasara wajen matsa lamba kan INEC domin ɗaukar matakin da ba bisa ka’ida ba, yanzu sun sauya dabara.

Rahotanni sun nuna cewa ana shirin shirya zanga-zanga a gobe Alhamis, 2 ga watan Afrilu a Abuja, wanda ake zargin wani minista mai ƙarfi ne ke daukar nauyinsa.
ADC ta ce manufar zanga-zangar ita ce:

Tara mutane da aka biya kuɗi
Su fito suna nuna kamar mambobin jam’iyyar ne masu fushi

Su rika kiran a cire David Mark daga shugabanci

A cewar jam’iyyar, ana son hakan ne domin a ƙara matsa lamba ga shugaban INEC ya amince da wani da ya riga ya ajiye mukaminsa kuma aka kore shi daga jam’iyyar.

Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa wannan yunkuri wata hanya ce ta APC domin kwace shugabancin jam’iyyar, wadda ta ce ita ce babbar jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a yanzu.

Sun kuma yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da waɗanda suke aikata wannan shiri idan ba da izinin sa aka yi ba.

ADC ta jaddada cewa za ta ci gaba da bin doka, amma ba za ta lamunci duk wani yunƙurin tauye dimokuraɗiyya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here