Home Siyasa ADC: Kamfanin shiga tsakanin Amurka da ƙasashe ya magantu kan INEC

ADC: Kamfanin shiga tsakanin Amurka da ƙasashe ya magantu kan INEC

4
0

Da ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Trump ba kamar irin Gwamnatin Joe Biden bace dole za’a dauki mataki kan hukumar Zaɓen INEC da gwamnatin Nageriya – Kamfanin shiga tsakanin Amurka ka kasashe ya magantu kan INEC

Wani kamfanin bada shawara da aikin lobbiyanci a Amurka mai suna Von Batten-Montague-York wanda ke aiki tare da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya fitar da gargaɗi mai ƙarfi ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC), kan zargin tabarbarewar sahihancin zaɓe a ƙasar.

A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a ranar 8 ga Afrilu, 2026, ya ce duk da goyon bayan da INEC ke samu daga Amurka da Tarayyar Turai, har yanzu akwai gibi mai yawa wajen tabbatar da zaɓe nagari, musamman idan aka fuskanci yunkurin magudi daga wasu ‘yan siyasa.

Kamfanin ya tuno da kura-kuran da suka faru a zaɓen 2023, yana mai cewa alamun irin wannan matsala na sake bayyana a halin yanzu.

Tun farko dai kamfanin ya kulla yarjejeniya da wani ɗan siyasa, Fabiyi Oladimeji, domin wakiltar Atiku Abubakar wajen shafar ra’ayin masu tsara manufofi a Amurka, da kuma kalubalantar labaran da gwamnati ke yadawa.

A cikin bayanin, kamfanin ya bayyana cewa yana shirye-shiryen ganawa da manyan ‘yan majalisar dokokin Amurka da kuma jami’an tsaro na ƙasa domin gabatar da rahoto kan halin da ake ciki a Najeriya.

Sun kuma jaddada cewa, sabanin gwamnatin Joe Biden da ba ta dauki mataki a 2023 ba, gwamnatin shugaba Donald Trump ba za ta zuba ido ba idan aka ga ana lalata tsarin dimokuraɗiyya.

Kamfanin ya yi barazanar cewa zai ba da shawarar a kakaba takunkumin Global Magnitsky ga duk wani ɗan siyasa ko jami’in INEC da aka samu da hannu wajen magudin zaɓe. Wannan takunkumi zai haɗa da:

Daskarar da kadarorin waje
Hana shiga tsarin kuɗaɗen duniya
Haramta tafiye-tafiye ga mutum da iyalansa

Haka kuma, kamfanin ya nuna damuwa kan matakin da INEC ta ɗauka na dakatar da amincewa da shugabancin jam’iyyar ADC, wanda ya dakatar da ayyukan babbar jam’iyyar adawa a daidai lokacin da ake shirin babban zaɓe.

A cewarsu, wannan mataki na iya kawo cikas ga damar jam’iyyun adawa su shirya tare da shiga zaɓe yadda ya kamata, lamarin da ke iya shafar dimokuraɗiyya a ƙasar.

Masu sharhi na ganin cewa, idan aka aiwatar da irin waɗannan takunkumi, zai iya yin tasiri sosai ga wasu jami’an Najeriya, musamman ma waɗanda ake zargi da hannu wajen rikita tsarin zaɓe.

Shin wannan gargaɗi zai sa a gyara tsarin zaɓe, ko kuwa zai ƙara rikita siyasar Najeriya? Lokaci ne kaɗai zai bayar da amsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here