Adam A. Zango ya girgiza Kannywood ya zayyano wadanda ya taimaka da dalilinsa na auri saki
Jarumi Adam A. Zango ya fallasa dalilansa na yawan sakin auren da yake yi.
A sakon da ya wallafa a sahihan shafukansa na Instagram da Facebook ya zargi tsofaffin matansa da aikata manyan laifuka.
Tun kafin ya fitar da wanann sako dai Zango ya yi gargaɗi a shafinsa na TikTok cewa kar wanda ya kuskura ya soma cewa da shi ba girmansa ba ne don ya yi tonon silili.
A baya-bayan nan dai Zango ya shiga cece kuce a Social Media tun bayan rasuwar Jaruma Daso har ma suka yi musayar kalamai da Dan TikTok ɗin nan da ake kira Dr. Hussaini Kano wanda ya ke zaune a kasar Libiya.
Dama tun a can baya Zango ya sha yin barazanar yin tonon silili yana mai cewa mutane ba su san fa hakurin da yake yi ba.
Tuni dai wannan tonon silili mafi girma da Zangon ya yi ya zama babban abin tattaunawa a kafafen sada zumunta.
Har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto babu ɗaya daga cikin tsoffin matan nasa da suka yi martani a kai.
Yanzu haka dai Jarumi Adam Zango yana can ƙasar Ghana inda ya ke gabatar da wasan Sallah, kuma rahotonni ya ce ya samu gagarumar tarba a can.