Abubuwan Da Suka Bayyana A Haduwar Bafarawa Da Ahmad Aliyu 

Abubuwan Da Suka Bayyana A Haduwar Bafarawa Da Ahmad Aliyu 

Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya hadu da tsohon Gwamna Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa a wurin sallar jana'izar surukinsa Alhaji Mamman Nasarawa waton mahaifin matarsa Hajiya Jamila Bafarawa.

Gwamna Ahmad Aliyu bayan kammala sallar janaza ya yi gaisuwar ta'aziya ga tsohon Gwamna in da ya samu zuwa har gidansa bayan kammala.salla a masallaci Sarkin Musulmi Muhammad Bello dake birnin jiha.

Haduwar shugabannin biyu ya nuna a Sakkwato ana siyasa ba da gaba ba Wanda hakan na iya haifar da cigaba a jiha.

Haduwar ta fito da yanda ake girmama juna a tsakanin shugabanni a jiha.

Haduwar ta fito da cewa akwai abubuwan da ke iya faruwa a jingine siyasa a gefe domin a tukari lamarin.