Abubuwa Biyu Da Ke Haddasa Gurɓacewar Tarbiyar Mace A Wannan Zamani

Kwadayi yana daya daga cikin matsalolin al'umma, kuma ya taka rawa wurin halakar da daruruwan mutane a duniya, hausa na cewa "KWADAYI MABUDIN WAHALA"  bahaushe yayi gaskiya, saboda duk wanda ya hau motar kwadayi zai sauka a tashar wulakanci ne! Matan wannan zamani kwadayi shine babban abokin su, shine mai daraja ta farko wanda ke dawainiya da rayuwar su,kuma shine mai dode duk wata jijiya mai isar da jinin tunani,da hangenn abinda kanje ya dawo wata rana.

Abubuwa Biyu Da Ke Haddasa Gurɓacewar Tarbiyar Mace A Wannan Zamani
Abubuwa Biyu Da Ke Haddasa Gurɓacewar Mace A Wannan Zamani
Abubuwa Biyu Da Ke Haddasa Gurɓacewar Mace A Wannan Zamani
:KWADAYI: Kwadayi wata kalma ce, wadda ake amfani da ita wajen bayyana kai makura ga son wani abu, ko bukatuwa da son abin wani.
Kwadayi yana daya daga cikin matsalolin al'umma, kuma ya taka rawa wurin halakar da daruruwan mutane a duniya, hausa na cewa "KWADAYI MABUDIN WAHALA"  bahaushe yayi gaskiya, saboda duk wanda ya hau motar kwadayi zai sauka a tashar wulakanci ne!
Matan wannan zamani kwadayi shine babban abokin su, shine mai daraja ta farko wanda ke dawainiya da rayuwar su,kuma shine mai dode duk wata jijiya mai isar da jinin tunani,da hangenn abinda kanje ya dawo wata rana.
Idan mace nada kwadayi takan kasance kamar wata dabba ce,wadda za'a ba ruwa akan turken tana mai tsananin jin yunwa.
     Yayin da 'ya mace ta kasance kwadayayya  to a sannan ne zata samun gurbataccin abokan shawara,tare da muradin wawasar abin hannun mutane musamman maza Masu ra'ayin mu'amala da mace irinta mai kwadayi.
 Yayin da idanuwanta za su makance su rasa ganin wane rame ne a gabanta.
 Komai iimin mace idan ta nada kwadayi to tana cikin babbar matsala.kwadayi shi ke haifar da roke-roke.
Shi kuma roko shike sanya tunanin "ban gishiri in baka manda"
:SAKI
A saki fa,kila kuyi mamakin dalilin daya sa na sanyo saki acikin jerin abubuwan da ke rusa tarbiya da tsari irin na mace.
Tabbas saki ya jefa da yawan mata acikin matsalolin rayuwa da damuwoyi masu yawa da illatarwa ga al'umma.
 
Kowa yasan saki halattacen abu ne,amma abune mai wanda mahalicci ya kyamata,amma ahakan kullum ta Allah ana samun mutuwar aure musamman a arewacin najeriya sama da 10.
Saki ya taka muhimmiyar rawa wajen kara gurbacewar tunanin 'ya mace yayin da ya kara raunatar da ita akan raunin da take da shi.
A wannan zamanin ne namiji kan saki mace da 'ya'yan da na kai 2 ko 3 koma fiye da hakan,kuma yayi karfin halin da ya barta da su,ba ci ba sha! Bare ayi maganar wani abu na jin dadin rayuwa.
Uwar ce zata dauki dawainyar wadannan 'ya'yan, mafitar ta daya ce idan ta nada sana'ar yi ko wani aikin wanda zai taimaka mata ga taimakin 'ya'yan ta.
Idan kuma akayi rashin sa'ar da ba tada sana'ar rike wadannan 'ya'yan ko kuma iyayenta ba su da karfin taimakon ta ita da 'ya'yanta,to daga nan ne zata fara tunain mafita akan yadda za'ayi ta taimaki 'ya'yanta da aka barta da su
Kula tana tsoron mayar da su agidan mahaifin su,gudun kada takura da bakar tsangwama su sanya su a gaba,har su kai ga shiga  cikin wani yanayi na "dauki ba a baka ba" ko kuma wani abu mai kama da wannan na Allah wadai. Duba da yadda wata bakar al'ada da ke kara ta'azzara acikin kasar hausa
'Ya'yan mace sakakkiya ba su da wata gata ko cikakkiyar kauna,saboda su din ba su da uwa acikin gida.
Da yawa namiji kan saki mace kuma shi ke nan zai barta da 'ya'ya,duk da yasan shine wanda aka dorawa nauyin su akan sa,amma sai yayi biris.
  Ita kuma mace ganin haka,zata iya afkawa acikin ko wace irin harkalla domin ta inganta rayuwar 'ya'yan ta.
Sau da yawa irin wadannan matan na afkawa cikin biye-biyen maza,domin su samu taro da sisin da za su sayi abin kaiwa a bakin salati.
   
Allah  sa mu da ce.
ZAINAB ALIYU SIFAWA.