Home Siyasa Abinda Yasa Gwamna Abba Ke Tsoron Komawa APC, Shehu Sani Ya Tono...

Abinda Yasa Gwamna Abba Ke Tsoron Komawa APC, Shehu Sani Ya Tono Abinda Ke A Ɓoye!

3
0

Abinda Yasa GwamnaAbinda Yasa Gwamna Abba Ke Tsoron Komawa APC, Shehu Sani Ya Tono Abinda Ke A Ɓoye! Abba Ke Tsoron Komawa APC, Shehu Sani Ya Tono Abinda Ke A Ɓoye!

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilan da suka sa ake ganin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ke jan kafa kan rade-radin sauya shekarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Shehu Sani ya ce sabanin sauran jihohin Najeriya inda sauya sheka ke faruwa cikin sauƙi, siyasar Kano ta bambanta, domin ta ginu ne a kan dogon tarihi na rikici, hamayya da akida, wanda ke sanya duk wani babban sauyin siyasa ya kasance mai matuƙar wahala.

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026.

A cewarsa:
“Duk sauya shekar da ake yi a ƙasar nan suna faruwa ne cikin sauƙi, amma banda ta Kano. Siyasar Kano har yanzu tana da zafi kamar yadda take a shekarar 1979.”

Shehu Sani ya yi waiwaye zuwa lokacin Jamhuriya ta Biyu, inda ya tuna da rikicin siyasa tsakanin jam’iyyun PRP da NPN, musamman a jihohin Kano da Kaduna. Ya ce rikicin akida da rabuwar kai a wancan lokaci sun girgiza siyasar Arewa, kuma har yanzu tasirin hakan yana bayyana a yau.

Ya kara da cewa rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar PRP a wancan lokaci ya jefa magoya bayanta cikin rudani, lamarin da ya yi kama da halin da siyasar Kano ke ciki a yau.

“Lokacin da PRP ta kasu kashi-kashi, mun shiga rudani, ba mu san bangaren da za mu mara wa baya ba,” in ji Shehu Sani.

Tsohon sanatan ya kuma ambaci yadda tsige marigayi Balarabe Musa daga kujerar gwamnan Kaduna ya karya gwiwar masu kishin tafiyar a wancan lokaci.

Da yake kwatanta wancan zamani da halin da ake ciki yanzu, Shehu Sani ya ce siyasa fasaha ce ta jure matsin lamba da tsallake ƙalubale, wadda ke buƙatar jarumta da zuciya mai ƙarfi.

A halin da ake ciki, jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa ba ta firgita da yiwuwar ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf ba, tana mai cewa ta riga ta gina ingantaccen tsari da zai ba ta damar lashe zaɓen gwamna a Kano a 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here