Abin Da Za'a Yi Jami'an 'Yan Sanda Su Daina wuce Gona Da Iri Yayin Aikinsu-----Hukumar Kare Hakkin Bil'adama

Abin Da Za'a Yi Jami'an 'Yan Sanda Su Daina wuce Gona Da Iri Yayin Aikinsu-----Hukumar Kare Hakkin Bil'adama
 

Daga Jabir Ridwan

 

A kokarin ta na magance matsalar muzgunawa da keta hakken bil'adama da jami'an 'Yan sanda ke yi, hukumar kare hakken bil'adama ta kasa hadin guiwa da gidauniyar MacArthur da sauran hukumomi masu zaman kansu sun shirya taron karawa juna sani na kwanaki biyu ga jami'an 'Yan sanda jahohin sokoto da kebbi da Kuma jahar Zamfara.

 
Taron Mai manufar ilmantar da jami'an 'Yan sanda hanyoyin gudanarda aikinsu ba tare da ketare iyaka ba, zai karade daukacin jahohi 36 dake fadin kasar nan.
 
Da yake zantawa da manema labarai sabon kwamshinan 'Yan sanda na jahar Sokoto CP Usman Muhammad ya ce ba shakka wannan akwai bukatar hukumomi masu zaman kansu su bayar da gudumuwa wajen gyaran ayukkan jami'an Yan sanda domin a magance matsalar da ake  fuskanta.
 
"Sanin kowa ne cewa a halin yanzu Nijeriya tana gudanarda harkar dimukuradiya Kuma babban adon demokradiya shi ne kare hakkin Dan Adam, haka Kuma yakamata mutane su san cewa akwai doka, su fahimci dokar nan an yi ta ne don jindadin su kuma hakkinsu  ne na kiyayeta".
 
Yakara dacewa kaucewa doka yakan sa abubuwa su tabarbare, idan Kuma kowa ya kiyaye doka, to ba shakka za'asamu kaykyawan tsaro da zaman lahiya kazalika Kuma kowa zai gudanarda lamurranshi cikin jindadi", a cewarsa.
 
Shima da yake bayyana alfanun taron ga jami'an 'Yan sanda, jami'in hukumar kare hakkin bil'adama ta kasa reshen jahar sokoto Halilu Ahmad Tambari cewa yayi lokaci yayi da jami'an za su san cewa ko Mai laifi yanada hakkin shi matukar ba kotu ta tabbatarda laifinsa ba.
 
"Wannan taron mun yi shi ne don Kara karfafawa jami'an 'Yan sanda tare da wayar musu da Kai Kam yadda za su gudanar da aikinsu ilmance batare da wuce iyaka ba.
 
"Kuma muna so mukara tunatarda su cewa mutane da suke tsarewa suma Sunada hakkinsu, Kuma Muna so jami'an 'Yan sanda su kasance suna aikinsu kamar yadda doka ta tanada, hakama Muna so yakasance idan akace wannan police station ce Tau ace tanada isassun kayan aiki da suka kunshi na'urar binciken sirri, na'ura Mai daukar hoto cikin sirri da dai sauransu kayan da suka shafi aikin 'Yan sanda",  inji Halilu Ahmad.
 
Masana nacigaba da alakanta rashin biyan jami'an 'Yan sanda hakkokinsu da matsalar wuce gona da iri da ake zargin su da yi a matsayin ummul'aba'isi na daukacin matsaloli da aikin yake fuskanta.
 
Taron dai ana San ran yakarade daukacin jahohi 36 dake fadin kasar nan harda birnin tarayya Abuja inji Halilu Ahmad.