Abin Da Ya Sa Shugaban APC Na Kasa Ya Yi Murabus
Shugaban jam’iyyar, APC, na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya mika takardar murabus dinsa a daren jiya Lahadi, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Majiya mai tushe ta tabbatar wa da Daily Trust cewa Adamu, wanda ya zama shugaban jam’iyyar na kasa a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a watan Maris din shekarar 2022, ya aike da takardar murabus din nasa zuwa fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja gabanin dawowar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga taron kungiyar tarayyar Afrika (AU) da ke gudana a Kenya.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce, Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, ya aike da wasikar murabus din ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da misalin karfe 4 na yammacin jiya Lahadi.
Har ila yau, wata majiya ta kusa da Adamu ta tabbatar da hakan, inda ta kara da cewa, “Shugaban jam'iyyar na kasa ya yi murabus ne biyo bayan samun labarin cewa wasu gungun ƴan jam'iyyar da ke kusa da shugaban kasa na wani shiri domin kunyata shi a taron jam’iyyar da za a yi gobe Talata da Laraba.”
Sai dai majiyar ta musanta wani rahoto da ke cewa shugaba Tinubu ne ya bukaci Adamu ya yi murabus gabanin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar na kasa da za a yi gobe Talata da Laraba.
Ɗaya daga cikin kusoshin da su ka kafa jam’iyyar ya ce Adamu ya yi murabus ne a lokacin da ya samu bayanin ccewa wasu mutane biyu masu fada a ji a kusa da shugaban kasar na ƙulla makirci a kansa kafin tarukan.
“Ya yi murabus ne saboda sun fara kitsa yadda za a tsige shi a tarukan masu zuwa. Ya yi murabus ne domin ya tsira da kansa daga wulakanci,” in ji babban dan siyasar.
Da aka tuntubi Adamu, ya shaida wa jaridar cewa ba zai ce uffan ba kan lamarin har sai Shugaba Tinubu ya dawo daga taron na AU.
managarciya