Abin Da Ya Sa Sanatoci Suka Ki Tabbatar Da El-Rufa'i Ya Zama Minista

Abin Da Ya Sa Sanatoci Suka Ki Tabbatar Da El-Rufa'i Ya Zama Minista

Majalisar Dattawan Najeriya ta ƙi tabbatar da tsohon Gwamnan Kaduna a matsayin minista kamar yadda Shugaba Tinubu ya nema.

Sauran mutum biyu da majalisar ba ta tabbatar ba su ne Sani Abubakar Danladi daga jihar Taraba, da kuma Stella Okotete ta jihar Delta.

Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya ce suna jiran rahoton jami'an tsaro kafin su tabbatar da mutanen uku.

Su kaɗai ne ba su shiga cikin mutum 45 ba da majalisar ta tabbatar a yau Litinin, amma ta tantance su tun daga Litinin da ta gabata da suka fara zaman.

Abin jira a gani rahoton jami’an tsaro zai zo da zargin aikata laifi ne ko akasin haka, amma dai kudirin majalisa na nuni da cewa komai zai iya faruwa kan mutum ukun da bas u tantance ba.