Home Manyan Labaru Abin da ya faru a hatsarin mota ga ‘yan jarida a Bauchi

Abin da ya faru a hatsarin mota ga ‘yan jarida a Bauchi

4
0

Wasu ’yan jarida da ke aikin aika rahoto a bikin kaddamar da ayyuka na hukumar raya Arewa maso Gabas (NEDC) a Jihar Bauchi sun jikkata a ranar Juma’a sakamakon wani hatsarin mota.

’Yan jaridan, da suka fito daga kafafen watsa labarai daban-daban, suna cikin tawagar NEDC ƙarƙashin jagorancin Ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Uba Maigari, domin miƙa ayyukan da aka kammala ga Gwamnatin Jihar Bauchi.

Hatsarin ya faru ne a kan hanyar Yashi–Yelwan Duguri da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri, jim kaɗan bayan da tawagar ta kaddamar da aikin Gidan Karatu na Sakandare na Gwamnati a Yelwan Duguri.

Rahotanni sun ce ’yan jarida da masu ɗaukar hoto da dama sun samu raunuka daban-daban a hatsarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here