Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da tsohon Sanata Kabiru Marafa da dukkan magoya bayansu sun bar jam’iyar APC zuwa jam’iyar PDP.
Shugaban jam’iyar PDP a Zamfara Kanal Bala Mande ne ya fitar da sanarwa bayan wani zama da suka yi na shugabanni a jiha in da suka aminta da shigar jagororin.
Ya ce bayan uwar jam’iyar PDP ta amince da shigowar tsohon gwamna da magoya bayansa haka suma a matakin jiha sun amince da shigowar domin a yi tafiya daya har a samu nasara a zabe mai zuwa na 2023.
Kafin wannan lokacin an yi ta rade-raden shigowar tsohon gwamnan abin da ya sha karyatawa kafin yanzu da aka bayyana shigowarsa a hukumance.
APC a Zamfara ana ganin ta yi hasarar rasa wannan jagoran siyasa da yake da dimbin magoya baya a jihar ta Zamfara.





