Abdul'aziz Yari Da Ahmad Lawan Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
Shugaban majalisar Dattijai Sanata Ahmad Lawan ya yi ganawar sirri da tsohon gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar a birini Abuja.
Ganawar wadda ba a bayyana yanda take ba da abin da ta ƙunsa ba amma dai a hasashen Managarciya tana da nasaba da siyasa.
A bayanin da wani makusanci ga Yari ya wallafa a turakarsa ya nuna ganawar an yi ta ne a tsakanin su uku ciki har da Sanata Mohammad Sani Musa.
managarciya