A na yi mu na jin daɗi', APC a tsakani PDP yayin da rikici ke ƙara ruruwa a jam'iyyar adawar

A yayin da ake fama da rikicin shugabanci a babbar jam’iyyar PDP adawa PDP, jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana jam’iyyar adawa a matsayin wacce ba za ta iya tafiyar da komai ba.
Jam’iyyar APC ta ce PDP ba ta tabuka komai ba banda lalata ƙasa a shekaru 16 da ta yi ta na mulkin Najeriya, inda ta ce jam’iyyar na fuskantar ɓacewa a ban-ƙasa.
Kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya ce PDP ba ta iya magance matsaloli na ciki da wajen jam'iyyar, in da ya ƙara da cewa "ana yi mu na jin daɗi"
“Najeriya har yanzu na fama da baƙin mulkin PDP na tsawon shekaru 16. Wannan jam'iyyar ta tafi. To wadannan taron tsintsiya ba sharar ne ke shirin sake mulkin kasar nan? Ku yarda da ni, wannan rikicin nasu ma ai somin-taɓi ne. Mu a jam’iyyar APC muna jin dadin wannan dambarwa," in ji shi.