A Mana'antar Shirya Finafinnan Hausa Ne Za Ka Samu Wadanda Iyayensu Sun Kasa Kula Da Su----Sarkin Waka

A Mana'antar Shirya Finafinnan Hausa Ne Za Ka Samu Wadanda Iyayensu Sun Kasa Kula Da Su----Sarkin Waka

Sarkin Waka Naziru Ahmad ya yi wa 'yar wasan Hausa martani kan kalamanta na nuna almajirai ne yaran da iyayensu suka haifa suka kasa kula da su, in da ya ki aminta da zancenta kuma ya bayyana mata in da ake samun wadan da aka haifa aka kuma kasa kula da su.

Sarkin waka ya nuna mata masana'antar da take ciki take bugun gaba da ita waton wurin shirya wasan kwaikwayo anan neake da wadan da iyayensu suka kasa kula da su

"Ba Almajirai Ne Iyayensu Suka Haife Su Suka Kasa Kula Da Su Ba, Idan Kana Neman Wadanda Iyayen Su Suka Haife Su Suka Kasa Kula Da Su To Ka Zo Masana'antar Finafinan Hausa,"  Martanin Naziru Sarkin Waka Ga Nafisa Abdullahi.