A Kwana 100 Na Mulkinsa Ahmad Aliyu Ya Yi Alkawalin Gyara Hanyayar Da Tambuwal Ya Kasa Gyarawa A Sokoto

A Kwana 100 Na Mulkinsa Ahmad Aliyu Ya Yi Alkawalin Gyara Hanyayar Da Tambuwal Ya Kasa Gyarawa A Sokoto

 

A lokacin da zaben 2023 ke kara karatowa da yawan magoya bayan jam'iyar PDP a jihar Sakkwato suna barin jam'iyar saboda ta kasa a kowane bangare kamar yadda masu sauya shekar ke fadi.

Dan takarar Gwamna a jam'iyar APC a jiha  Honarabul Ahmad Aliyu Sokoto ya yi alkawalin zai gyara hanyar Huchi dake cikin karamar hukumar Wurno wadda ambaliyar ruwa ta lalata  shekarun da suka gabata, a cikin kwana 100 na farkon mulkinsa matukar aka zabe shi gwamnan Sakkwato a 2023.

"font-family: times new roman, serif;">Ahmad Aliyu ya furta hakan ne a karamar hukumar Wurno a lokacin da yake karbar mutanen da suka sauya sheka daga PDP zauwa APC su 4,270.

Ya nuna gamsuwarsa kan yadda ake shigowa jam'iyarsu kan haka ya yi kira ga sauran wadan da ba su shigo APC ba da su zo a kafa sabuwar Sakkwato da za ta samar da ruwan sha da kula kiyon lafiya da hanyoyin mota a jihar.

Ahmad Aliyu amadadin jagoran jam'iyar APC a Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya tabbatarwa wadan da suka sauya shekar za a yi tafiya tare da su ba nuna bambanci.

Ya ce in aka zabe shi gwamna zai cigaba da aiyukkan alheri daga in da Sanata Wamakko ya tsaya.

"jam'iyar PDP ta kasa gaba daya ba alkawalin da ta cika wanda ta yi wa mutanen jihar Sakkwato don haka akwai bukatar canji a jiha", a cewarsa.

Shugaban jam'iyar APC Honarabul Isah Sadik Achida a lokacin da yake maraba da wadan da suka shigo jam'iyar ya ce a shirye jam'iya take domin a yi tafiya tare don samar da nasara a kowane mataki.

A bayanin da Bashar Abubakar mataimaki na musamman kan kafofin sadarwa na zamani  ga Sanata Aliyu Wamakko ya fitar ya ce masu sauya shekar sun yanke shawarar ne domin rashin alkibla da makama a jam'iyar PDP a jihar Sakkwato.

Ya ce a garin Achida akwai mutum 1,400 da suka shigo APC, haka ma a karamar hukumar Kware akwai 1000 da aka karba domin aminta da tafiyar Sanata Wamakko.