Aƙalla Mutane 50 Za su Amfana Da Horo Kan Kafa Masana'antu Da  Sana'oin Hannu a Jihar Sakkwato

Aƙalla Mutane 50 Za su Amfana Da Horo Kan Kafa Masana'antu Da  Sana'oin Hannu a Jihar Sakkwato

Hukumar samarda ayukkan Yi ta kasa ta bayyana cewa  zata koyama matasa 50 Sana'oin hannu dama dabarun  Kafa masana'antu domin nan gaba suma su iya Bada tasu gudumuwa wajen raya kasa.

Darakta Janar na hukumar Abubakar Nuhu Wanda jami'ar hukumar a nan jahar Sokoto ta wakilta Eunice Dan Malam ta wakilta, shine ya bayyana hakan a yayin soma horon na wuni biyar.

Yace horon zai Bada dama ga wadanda suka kammala karatu Amma Basu da aikin yi sukasance masu iya dogaro da kansu ta hanyar sana'ar da suka koya.

Eunice Dan malam ta bukaci masu hannu da shuni dama masu masana'antu masu zaman kansu dasu Bada gudumuwa matuka domin a yaqi matsalar rashin aikinyi Dake addabar matasan kasar nan.

Idan dai za'a iya tunawa Gwamnatin tarayya ta fito da shiraruka daban daban domin ceto matasan kasar nan daga halin da suke ciki na matsalar rashin aikinyi  Wanda zasu dogaro da kansu a daukacin fadin kasar nan.

Wasu daga cikin wadanda zasu amfana da horon sun bayyana gamsuwa da irin yadda tsarin horon zai kasance inda suka yabama hukumar tareda fatan samun ire iren wannan damar ga daukacin matasan kasa Baki daya.