Kwamishiniyar Muhalli Ta Jihar Gombe Ta Yi Murabus
Kwamishiniyar muhalli ta Jihar Gombe, Dakta Hussaina Goje ta ajiye muƙaminta na Kwamishiniyar muhalli da kula da gandun daji a jihar.
Kwamishiniyar ta ajiye aikinta ne saboda wasu dalilai na ƙashin kanta
Managarciya na hasashen murabus nata nada nasaba da rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin tsohon gwamna Danjumma Goje da Gwamna Inuwa Yahaya a kwanannan.
Siyasa ta fara zazafa a jihar biyo bayan bambancin ra’ayin da ya kunno a siyasar jihar.





