Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana alhini da jimami kan rasuwar wasu ‘yan wasa daga jihar Kano sakamakon mummunan hadarin mota da ya auku a ranar Asabar.
Lamarin ya faru ne a yayin da tawagar ‘yan wasan jihar ke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala kwanan nan a Jihar Ogun.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a yau Asabar.
“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar, da kuma masu ruwa da tsaki a fannin wasanni a jihar Kano da Najeriya baki daya.
“Muna rokon Allah Ya jikan ‘yan wasan da suka rasu, Ya kuma ba iyalansu hakuri da juriyar wannan babban rashin,” in ji AbdulRazaq.





