Ganduje Ya Ba Da Kyautar Miliyan 10 Don Gina Makarantar Islamiyya
Gwamnan Jihar Kano, Drakta Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci bikin saukar karatun Al-Qur’ani Mai Girma na dalibai 235 na Madrasatul Babban Malami na Madabo har ya ba da tallafin cigaba da aikin makarantar.
Bukin wanda aka gudanar a dakin taro na GSS Gwammaja dake karamar Hukumar Dala a birnin jiha.
Mai Girma Gwamnan ya ba da tallafin kudi Naira miliyan Goma domin cigaba da ginawa makarantar mazaunin ta na dindindin.
Shugabanni da daliban makarantar sun yabawa Gwamnan bisa y dawainiya da harkokin addinin Musulunci musamman a wannan makaranta in da suka masa karramawa ta musamman.





