Home Uncategorized Ciyamomin PDP na Jihohi 36 Sun Yanke Shawara Kan Kujerar Damagum 

Ciyamomin PDP na Jihohi 36 Sun Yanke Shawara Kan Kujerar Damagum 

7
0

Muƙaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum ya jagoranci wani muhimmin taro da shugabannin jam’iyyar PDP na jihohi 36 a ranar Laraba a Abuja.
Wannan taro na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar PDP ke shirye-shiryen taron majalisar zataswa (NEC) ta kasa wanda za a yi ranar 28 ga watan Nuwamba. 
Jaridar The Nation ta tattaro cewa taron ya gudana ne a hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza a Abuja ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024. 
A wurin wannan taro, Damagum da ciyamomin PDP na jihohin Najeriya sun musanta raɗe-raɗen cewa shugaban jam’iyyar na fuskantar barazanar tsigewa.
Har ila yau, bayan taron ciyamomin jihohin sun jaddada goyon bayansu ga muƙaddashin shugaban PDP Umar Damagum.
A hira da aka yi da su, shugabannin sun bayyana babu wani abin damuwa ko barazana ga kujerar Damagum a taron NEC da ke tafe. 
A nasa jawabin, Damagum ya ce shugabannin PDP na jihohi sun kawo masa ziyara ne kamar yadda aka saba, saɓanin raɗe-raɗin da ake cewa ba su jituwa.
“Wannan taron ba sabo ba ne, dama mu kan haɗu mu tattauna a baya, ba yau ne karon farko ba, mun shirya wannan zama ne domin tattaunawa da ciyamomin jihohi. “Idan kuka duba galibin shugabannin jam’iyya na jihohi ba a daɗe da zaɓensu ba, kusan duk sababbi ne, don haka mun kira wannan zama ne mu san juna amma ba shi da alaƙa da NEC.” 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here