Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya yi gargadin cewa ba za a amince da kawo cikas ga harkokin tsaro a gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.
Ya bayyana haka ne a wajen taro da aka yi a Abuja ranar Laraba, inda ya jaddada aniyar shugaban kasar na kawar da ‘yan fashin daji, ‘yan ta’adda, da sauran matsalolin tsaro.
A cewar Ribadu, manyan tsare-tsare na gwamnati sun kai ga kashe daruruwan ‘yan bindiga a kullum, wanda ya tilastawa da dama yin gudun hijira zuwa kasar Chadi.
Ya ce shugaba Tinubu ba zai sassautawa duk wani mai kawo cikas ga tsarin kasa.





