Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Bulama Bukarti, ya bayyana cewa, kungiyar ta’addanci ta Lakurawa tana sa ido kan al’ummomi da sansanonin sojoji a yankin Arewa maso Yamma.
Bukarti, lauya mai kare hakkin dan Adam ne ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television’s Politics Today.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro Manjo Janar Edward Buba ya bayyana ‘yan ta’addan a matsayin wata kungiya da ta fito daga jamhuriyar Nijar, bayan wani juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa sa’o’i 48 bayan sanarwar da sojoji suka bayar, ‘yan ta’addan sun kai hari garin Mera da ke karamar hukumar Augie a jihar Kebbi, inda suka kashe akalla mutane 15.





