Bagudu ya aika sunayen Shugaba da mambobin hukumar zabe ga majalisar dokokin jiha
Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu a ranar Talata ya aikawa majalisar dokokin jihar sunayen shugaba da mambobinsa da yake son a tantance a kuma tabbatar domin su jagoranci hukumar zabe mallakar jiha.
A takardar da ya tura wadda mai baiwa gwamna shawara kan yada labarai Yahaya Sarki ya rabawa manema labarai a birnin Kebbi ya ce sunayen sun hada da Aliyu Muhammad Mera a matsayin shugaba, sai Ahmed Amadu Nasani, Mustapha Usman Ka’oje, Honarabul Aliyu Ahmed Adamu da Honarabul Sa’idu Moh’d Dankolo, dukansu mambobi ne a hukumar zaben.
Bagudu ya ce zabar mutanen yana kunshe ne a cikin daftarin doka sashe na 198 da kundin tsarin mulki wanda aka yiwa gyaran fuka a 1999.
Bagudu ya ce ya nada mutanen ne domin su taimaka masa ga hakkin da doka ta daura masa.





