•Yana hana warin jiki.
•Yana sa fuska, laushi da sheƙi na musamman.
•Yana goge taɓon fuska harda na gaɓɓai.
Zaki samu Lemon Tsaminki, ki goga a hamattanki, a lokacin da zaki shiga wanka. Ki barshi kimanin minti goma kamin ki wanke.
Ki haɗa ruwan Lemon Tsaminki da sugar ki dinga gogawa a fuskarki, ki sa ruwan ɗumi ki wanke.
Ki tanadi ruwan Lemon Tsaminki da Cotton kina gogawa a taɓon fuska ko gaɓɓan jiki, yana cire taɓon fuska da sa gaɓɓan haske na musamman.





