Home Siyasa Haɗaka:Seyi Makinde Ya Amince Ya Marawa Atiku Baya Domin Kayarda Tinubu a...

Haɗaka:Seyi Makinde Ya Amince Ya Marawa Atiku Baya Domin Kayarda Tinubu a Zaɓen 2027

6
0

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, na shirin bayyana tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa da yake son marawa baya a zaɓen 2027.

Rahoton ya bayyana cewa ana sa ran Makinde zai sanar da matsayinsa a hukumance tsakanin ƙarshen watan Nuwamba zuwa makonnin farko na watan Disamba na 2026.

Wannan mataki na siyasa ya biyo bayan makonni da dama na shawarwari da tattaunawa tsakanin wakilan manyan ‘yan siyasar biyu.

Tattaunawar ta gudana ne a daidai lokacin da wasu shugabannin jam’iyyun adawa ke duba hanyoyin haɗin gwiwa domin fuskantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

–MIKIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here