Tsohon Gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta kudu, Aminu Waziri Tambuwal, ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya yaba da gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa.
Tambuwal, a cikin saƙon taya murnar da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a matsayin mutumin da hidimarsa ga al’umma ke nuna jarumta, juriya, kishin ƙasa da dattako.
Ya yaba wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya, kare tsarin mulki da bin doka da oda, da kuma inganta haɗin kan ƙasa.
Tambuwal ya kuma yaba da jarin da Atiku ya zuba a fannonin ilimi, kasuwanci da bunƙasa ƙwarewar al’umma, yana mai cewa hakan ya samar da damammaki, ya sauya rayuwar mutane tare da zaburar da al’ummomi daban-daban na ‘yan Najeriya.
Da yake waiwayen gwagwarmayar siyasa da ta dimokuraɗiyya da suka yi tare, Tambuwal ya ce ya shaida da idonsa ƙarfin halin Atiku, karamcinsa da kuma jajircewarsa wajen ganin an samu Najeriya mai haɗin kai, zaman lafiya da wadata.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba Atiku lafiya, ƙarin ƙarfi da hikima, tare da tsawon shekaru domin ci gaba da yi wa Najeriya da bil’adama hidima.





