Shin ko samari da ’yan mata sun san cewa soyayya ta gaskiya ba wai furta kalaman Ina sonki ko Ina sonka kawai ba ce? Shin kun san cewa akwai wasu muhimman abubuwa da suke gina soyayya mai ɗorewa, wadda ba ta rushewa saboda ƙananan matsaloli?
Soyayya ta gaskiya tana buƙatar gaskiya, amana, haƙuri, fahimtar juna da kuma mutunta juna. Ba za ka ce kana son mutum ba alhali kana ƙoƙarin cutar da zuciyarsa ba, kana ɓoye masa gaskiya.
A matsayinki na budurwa, ki fahimci cewa ba duk wanda yake yawan furta kalaman soyayya ba ne yake da niyyar gina rayuwa da ke ba. Kada ki bari kyawawan kalamai su ruɗe ki har ki manta da lura da halayensa. Namiji mai sonki da gaske zai nuna hakan ta hanyar kulawa, mutuntawa, gaskiya da kuma tsayawa a kan maganarsa.
Haka nan kuma a matsayinka na saurayi, ka fahimci cewa mace ba ta buƙatar kyawawan kalamai kawai, tana buƙatar namijin da zai fahimce ta, ya saurare ta, ya girmama ra’ayinta, ya kula da damuwarta kuma ba zai mayar da hawayenta banza ba.
Wani babban sirrin soyayya shi ne iya tattaunawa a lokacin saɓani. Domin babu soyayyar da ba ta samun saɓani, amma abin da ke bambanta soyayya mai ƙarfi da wadda ba ta da tushe shi ne yadda masoyan suke warware matsalolinsu. Kada ku mayar da duk wani saɓani ya zama dalilin cin mutunci, zagi ko barazanar rabuwa.
Haka kuma, kada ku yi ƙoƙarin canza junanku ta hanyar tilastawa. Ku koyi karɓar juna, ku gyara kurakuranku cikin hikima, ku ba juna damar yin kuskure da kuma damar gyarawa.
Abu mafi muhimmanci shi ne, kada soyayya ta sa ka manta da mutuncinka da burinka. Soyayya ba bautar mutum ba ce, kuma ba lasisi ba ne na zaluntar wani.
A wannan gaɓar: Soyayya ta gaskiya ba a auna ta da yawan saƙonnin da kuke aikawa juna, tsawon lokacin da kuke waya ko yawan kyaututtukan da kuke yi wa juna. Ana auna ta ne da gaskiya, amana, mutunci, kulawa da kuma yadda kuke ƙoƙarin ganin junanku cikin farin ciki.
Samari da ’yan mata, idan kuna son soyayyarku ta zama mai ɗorewa, ku fara da zama abokan juna na gaskiya kafin komai. Domin kyakkyawar soyayya ba wai samun wanda za ka so kawai ba ce, samun wanda zai san darajar zuciyarka ne.
#Managarciya


