Daga Yahaya Mahi Na Malam Babba
‘Yan bindiga sun kai hari a Masallacin Malam Yahuza dake unguwar Low-Cost, a Kaura Namoda, a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu masallata a safiyar yau Lahadi.
Lamarin ya faru ne lokacin da ake cikin raka’a ta biyu kuma ta karshe ta Sallar Asuba, a lokacin da maharan suka afka wa masallacin.
Har zuwa lokacin hada wannan labari, ba a iya tantance adadin mutanen da aka yi awon gaba da su ba, sakamakon wasu masallatan sun watse domin tsira da rayukansu a lokacin harin.
Lamarin tsaro dai na ci gaba da ta’azzara a Kaura Namoda. Hakan na zuwa ne bayan da a safiyar jiya Asabar, maharan suka shiga unguwar Kofar Tsamiya, inda suka yi awon gaba da mutane hudu, wadanda har zuwa yanzu ba a san inda suke ba.
Duk da cewar hukumomin tsaro na cewa suna iya bakin kokarinsu na kawo karshen matsalolin tsaro a kasar baki daya, al’ummar yankin na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda hare-haren ke kara yawaita.





