Home Beauty & Personal Care Amfanin Gawayi Ga Fatar Ɗan Adam

Amfanin Gawayi Ga Fatar Ɗan Adam

3
0

Shin kin san amfanin Gawayi? Eh gawayi dai wanda muke hura wuta da shi domin samarwa kanmu abinci.

Ana amfani da shi wajen
Taimakawa wajen cire datti daga saman fata.
Rage yawan maiƙo a fuska na ɗan lokaci.
Tsaftace fata.

Ki niƙa gawayi ya zama gari mai ki tabbatar da ya yi laushi sosai.

Ki samu ruwan ɗumi ki zuba kan gawayinki, ki kwaɓa shi da ɗan kauri kauri ruwa ruwa, sai ki shafa a fuskarki na tsawon minti 5, Sannan sai ki wanke fuskar da ruwa masu tsafta.

Zaki iya haɗa gawayi da zuma kuma.

Ki zuba rabin cokali na garin gawayi, ki sa cokali ɗaya na zuma, sai ki gaurayasu waje ɗaya, Sannan ki shafa a fuska na minti 5–10.

Ka da ki yi amfani da gawayin da aka ƙona, ma’ana wanda aka fitar jikin itace kai tsaye.

Ka da ki shafa kusa da ido, ki kiyaye
Kada ki yi amfani da shi kullum, ki ɗan dinga bayar da tazarar kwana ɗaya zuwa biyu kamin sake yin haɗin.

#Managarciya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here