Home Siyasa Taron APC a Kaduna ya nuna ‘yan Najeriya ba sa tare da...

Taron APC a Kaduna ya nuna ‘yan Najeriya ba sa tare da Tinubu – ADC

17
0

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya bayyana rashin gamsuwarsa da taron ƙaddamar da yakin neman zaɓen jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ya ce duk da cewa an tattaro mutane daga jihohi bakwai na shiyyar da ma wasu wurare, filin taron na filin wasa na garin Kaduna bai cika ba.

A cewarsa, lamarin ya nuna cewa jama’a ba su karɓi jam’iyyar APC da manufofinta yadda take tsammani ba. Ya kuma yi zargin cewa an biya wasu mahalarta taron kuɗi tsakanin naira 50,000 zuwa 100,000 domin halartar taron.

Ologbondiyan ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan halin tattalin arzikin ƙasar, musamman cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ƙara wa ’yan Najeriya wahalhalu.

Ya ce APC ta sake gabatar da alkawuran da ta saba yi a lokacin zaɓukan 2015, 2019 da 2023, ba tare da ta yi cikakken bayani kan nasarorin da ta samu a shekarun da ta yi tana mulki ba.

ADC ta buƙaci APC ta nemi afuwar ’yan Najeriya kan matsin tattalin arzikin da suke fuskanta, tare da shirin miƙa mulki a zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here