Mahara sun buɗawa ‘yan majalisa 3 wuta a Nasarawa
Wasu ‘yan majalisar jihar Nasarawa sun tsallake rijiya da baya yayin da mahara suka buɗe musu wuta.
Lamarin ya faru ne a daidai ƙauyen Wowyen dake kan titin Kwanga zuwa Lafiya dake jihar ta Nasarawa.
‘Yan majalisar da lamarin ya rutsa da su Samuel Tsebe, David Maiyaki da Peter Akwe, in da suke kan hanyarsu ta dawowa daga wajen wata jana’iza ne yayin da lamarin ya faru.
‘Yan majalisar sun tsallake rijiya da baya domin su fita da rayuwarsu.




