Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 14

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 14

23
0

Na 

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

PP 14

ƁANGAREN HALISA

Halisa da haushi ya gama ƙume ta ba ta sake cewa komai ba ta haye gado ta kwanta tana hasashen wa zai iya kasancewa munafukin nata a gida da kewaye. 

Zazzaɓin da ya fara lafa mata a da ne ya ƙara taso mata amma ba ta nunawa kakar ba tun da ta riga ta sha magani.

 Haka ɗanyar zuciyarta ta ci gaba da jinyar rashin Hayat da kuma ƙoƙarin ƙarfafa kanta don mantawa da shi sai dai ruwan hawaye bai dakatawa ɓulɓulowa daga rijiyar idanunta ba, saurin juyawa ɓangaren dama ta yi tana fuskantar bango saboda kada kowa ya fahimci halin da take ciki. A haka har shugaban barayi na duniya ya sace ta wato bacci.

 Ba ita ta farka ba sai da azahar ko da ta tashi ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai kuma sai ta ji ta a wartsake ba ciwon, wayarta ta janyo ta duba a gogo.

“Kai! Yau na sha bacci ba laifi.” Ta furta tana laluben inda ta ajiye uniform ɗin ta na islamiyya a cikin ƙaramar akwatinta, sai dai ba ta gan su inda ta ajiye ba. “Tofah, ko dai tsohuwar nan ce ta sake musu wuri?”

Ganin ba ta da mai ba ta amsa ta sauko ta fita waje da nufin neman kakar don ta tambaye ta kawai idonta ya sauka a kansu suna shanye a igiyar da ke tsakar gidan ƙarƙashin ice.

Ko da ta taɓa sun riga da sun bushe don haka ta kwashe su ta yi cikin ɗaki, ta fiddo dutsen guga daga ma’adanarsa. Akwai wuta shi ya sa tunanin yin gugar ya ɗarsam mata a rai, ta shimfiɗa sallaya da ɗankwalin atamfa sannan ta fara aikin.

Lokacin makarantar yana yi ta shirya da wuri kasancewar a ‘yanmatan gidan ba su fi su huɗu ba ne suke zuwa makarantar islamiyyar saura duk ta allo suke yi.

 A masu zuwan ma tana ɗaya daga cikin waɗanda sai sun ga dama suke zuwa don har ta fi shiri da ta boko, amma a wannan ranar haka kurum ta ji tana sha’awar zuwa duk da kuwa ko ta ƙi zuwan ba abin da zai faru,  idan ma kuma an yi mata magana tana da uzurin bayarwa.

Suna tafe kan hanya da ke a ƙafa suke tafiya makarantar, suka jiyo ana rangaɗa sallama a bayansu. “Assalamu alaikum ‘yanmata ji mana, da ku nake magana.”

Abinka da sha’anin ƙwaila sai ta ce da Sa’adatu “Kar mu juya mu ƙara sauri ma.”

Haka aka yi suka ƙara hanzarin tafiyar tasu amma ba su ji an daina bin su ba, a tare suka juyo suna kallon samari biyun da suka tabbatar ɗaya daga cikinsu ne ya dakatar da su.

Fara riƙe dariyarta ta yi tana raɗawa Sa’adatu magana a kunne. “Kin ga wani mai ranƙwalelen kai kamar taragon jirgi.”

Hannu Sa’adatu ta saka ta ture fuskar Halisa daga kunnenta murya a ƙasa sosai ta ce “Ki daina abin da kike yi, ba kyau zagin halittar Allah.”

Sannan ta ɗan ware muryarta daidai sautin mace ta ce da shi “Wa’alaikumus Salam, malam me ya faru kake dakatar da mu ba ka ga a hanya muke ba?”

“Na gani baiwar Allah ku yi haƙuri na dakatar da ku ne saboda idan kuka wuce ba mu san inda za mu sake haɗuwa ba. Wannan ƙawar taki ce za ki taimaka ki ba mu lambarta in ba damuwa.”

A lokacin dariya ta ƙwace mata za ta yi magana kenan Sa’adatu ta ja kafaɗarta ta juyar da ita gaba suka ci gaba da tafiya tana faɗar “Ku yi haƙuri za mu makara.”

“Number fa?”

“Ba ni da waya sai dai ko ita.”

Da ma tata muke nema don Allah a ba ni.” Ya buƙata yana ci gaba da biyo su. 

Cike da tsiwa Halisa ta kalli Sa’adatu ido cikin ido ta fara furzar da jawabanta na gargaɗi.

“Wallahi kar ki sake ki ba shi lambar ko da a ce kina da ita, ina zan kai wannan kayan ranƙwal ɗin, da ma na tare da shi ɗin ne da dama. A bar ni ma na ji da abin da ya dame ni ahto.”

Dafe kai Sa’adatu ta yi tana shakkar kada a ce bawan Allahn nan ya ji abin da Halisa ke faɗa don hakan ba zai masa daɗi ba.

Ba su sake juyowa ba ta ce da shi “Don Allah ku yi haƙuri ka daina biyo mu mun kusa ƙarasawa makaranta wani daga cikin malamai zai iya ganinmu ku ja mana hukunci.”

Dafa kafaɗar abokinsa ya yi yana ɗaga kafaɗa alamun ba komai ya ce

“Shi kenan, Al’amin ka yi haƙuri Allah ya ba ka wata a gaba.”

Da hanzari Halisa ta waigo don jin zancen da ya yi kaɗai ya tabbatar mata da cewa ɗan kyakkyawan ne ke son numberta ashe shi ne take ƙoƙarin yin saki na dafe.

Sai dai ta makara don juyowarta ya yi daidai da lokacin da suka juya suka fara tafiya. A wurin ta tsaya cak tana kallon bayansa, iya bayan idan ka gani za ka tabbatar ma’abocin jikin ya haɗu, ga shi ba damar ta dakatar da su, idan ta yi haka ajin da take ji tana da shi a matsayin ‘ya mace zai zube.

Sa’adatu har ta ɗan yi nisa kaɗan ta lura ashe abokiyar tafiyar tata ba ta tare da ita don haka ta waiga bayanta cikin tsoro zuciyarta na lugude. Sai kuwa ta hango ta can a tsaye ta juya baya. Da mamaki ta koma gun ta taɓa bayanta, ta waigo a ɗan firgice. Ganin ko wace ce ya sa ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tana furta “Kai haba! Kin tsorata ni wallahi.”

Sa’adatu ta amshe zancen da faɗar”Ai ke ce kika tsorata ni da na waigo ba kya gun ba ki ji bugun zuciyata ba, har na ji a raina kar dai a ce aljanu ne kika tsokana suka ɓace da ke.”

Dariya ta dinga yi suka kama hanya suna ci gaba da nufar inda suka saka niyyar zuwa tana faɗar “Ah haba dai! Sai kuma su tafi da ni a kan ɗan wannan abun?”

“Ke kika raina abin da kika yi, amma wani zai iya riƙe ki a rai tsawon zamani saboda wannan ɗin da kika raina. Haba! Tozarci ai ba shi da daɗi. Ba wannan ba ma me ya tsayar da ke.”

Da kamar za ta faɗa mata sai kuma ta yi tunanin shi ma yin hakan faɗowar ajinta ne idan aka gane ta damu da shi, gara dai ta haƙura ta bar wa ranta ai ciki ba don tuwo kawai aka yi shi ba har da adana magana, idan rabonta ne watarana za su sake haɗuwa.

Don haka ta nunawa ‘yar’uwar tata ai ba komai suka ci gaba da tafiya har suka shige makarantar.

Bayan kwana biyu da faruwar hakan ta kama ranar jumu’a bayan sun dawo daga makaranta ta fara shirye-shiryen fita, tana so ta je gidan mamanta da zarar an sauko daga masallacin juma’a, ba don ma ba za ta iya tafiya da uniform ba da daga can makarantar za ta wuce domin unguwar ba ta da nisa da makarantarsu. A lokacin da ta gama shiryawa kuma lokacin sallar ya riga ya yi ta tabbatar hanyar ba za ta biyu ba saboda akwai masallacin juma’a a hanyar, idan har tana son tafiya cikin daɗin rai dole ta jira a sauko. 

Ta aikata kamar yadda zuciyarta ta raya mata. Da ta zo za ta tafi ta kalli kakar “To Ige ni zan tafi kina da saƙon da zan kai wa mama?”

Ige ta taɓe baki tana ci gaba da kakkaɓe tabarmar da take “A’a in dai ke kina da shi ki ɗauka ki kai mata uwarki ce ba zan hana ki ba, amma ni dai ba dalilin da zan ba wa mai baƙin hali kayana.”

Turbune fuska ita ma ta yi ta kalli Ige kamar za ta yi kuka a shagwaɓe ta ce “Habah Ige! Yanzu uwar tawa kike zagi don kawai na miki zancenta?

“To ai ke ma kin ji me kika faɗa uwarki ce ba tawa ba. Ai kuma ban mata ƙarya ba ina ce saboda baƙin halinta da ƙyar ta yarda kika zauna a hannuna shi ma don Halilu ya fi ƙarfinta ne da a ce ɗan nawa ba tsayayye ba ne da tuni ta ƙwace mini ke. Ke ma rigima ce kawai take kai ki gun ta tun da duk kika je da ɓacin rai kike dawowa.”

Rai a jagule Halisa ta fara magana “To na ji dai abar maganar, don idan kika ci gaba da zaginta yasin daga wannan zuwan ba zan dawo wurinki ba.”

Ganin ta haɗe fuska ta sha mur alamun da gaske take ya saka tsohuwar ta sha jinin jikinta don ba ta ƙaunar ta ji ko an yi zancen nisanta ta da ‘yar cakwai da take matuƙar ƙauna, ƙaunar da ta samo asali daga kasancewarta takwara a gare ta shi ya sa  tun tana ‘yar shekara 6 da iyayen suka rabu ta karɓe ta daga hannun mahaifiyarta don kaf a jikokinta ba wacce take ji kamar ita. Tana da shekaru 8 Allah ya yi wa mahaifinta rasuwa, tun daga lokacin tausayin maraicinta ya sa kakar ta ƙara riƙe ta gam-gam ba ta yarda wani abu na ba daɗi ya same ta, idan so samu ne ko ƙuda ba ta so ya hau kan shalelen tata, idan kuwa tsautsayi ya sa ka shiga sabgar yar cakwai ka taro rigimar da ba za ka iya tarewa ba.

Da sanyin jiki ta furta “Shi kenan na daina ‘yar cakwaina, ki je Allah ya tsare ya dawo mini da ke lafiya. Don Allah kar ki kai dare kin ji? Kin san dai ba wani iya wayar na yi ba ballantana na kirawo ki na ji ko lafiya in kin jima.”

Gyaɗa kai ta yi alamar to ta ɗauki hijabinta kore ta ɗora a kan doguwar rigar yadi fara da kore da ke jikinta ta bi hanyar waje bayan ta karɓi ɗari bakwai a hannun kakar da sunan kuɗin abin hawa. Ita da kanta tsohuwar ta san kuɗin sun zarta na abin hawa, amma ba yadda ta iya tun da ba ta ƙaunar ɓacin ran jikar tata dole ta ba ta.

Ta yi nisa da gida sosai har saura kaɗan ta ƙarasa titi ta ci karo da wani yaron maƙotansu da suke ɗasawa da shi sosai a kan babur ya wuto yana ƙoƙarin fita titin. Ɗaga murya ta yi tana faɗar “Abdul! Abdul dakata!! Tsaya!”

Jin ana ta kwaɗa masa kira ya saka shi cin burki ya waigo fara’ar fuskarsa ta faɗaɗa “Ah’ah! Apsara tawa, guguwa abarki da Allah kowa kika kwasa ya ci ƙasa.” Hannu ta miƙa masa suka tafe tana dariya ta ce “Kai ma dai shegen bisan ne, ka iya ɗora mutum a network.” 

Shi ma dariyar ya yi yana mayar mata da “Ai kin kai hakan ne. Ina kika nufa?” Ya ƙarashe zancensa da sigar tambaya.

“Kai dai wai Minannata zani wallahi. Ko na hau ka rage mini hanya?”

Gyaɗa mata kai ya yi alamar eh yana faɗar “Mu je na sauke ki, gaban can na nufa.”

“To mu je, nisan kwana ai sai da gwaji.” Ta faɗa har a lokacin tana cikin fara’a.

Shi dai ba kodayaushe yake fahimtar ƙarin maganganunta da manyancenta wurin zance ba, kawai dai ya san hakan bai rasa alaƙa da tashinta a hannun tsofaffi.

Umurnin hawa ya ba ta, ta yi ɗal ta ɗale tana riƙe kafaɗunsa don ji ta yi kamar za ta tuntsiro ƙasa.

“Bi a hankali fa.” Ya furta a taƙaice bayan ta hau ya fara tafiya ne ya ji har a lokacin tana riƙe da shi ya ce “Habah Apsara sake ni mana kafin wani ya ganmu ki jefa ni a masifa.”

Ta yi hanzarin janye hannunta daga kafaɗun nasa. “Yi haƙuri na riƙe ne gudun faɗuwa, amma me zan ji a jikin naka?” Ta harari bayan ƙeyarsa.

Ta mayar da hannun baya ta riƙe ƙarfen gefen seat sosai tana jan gajeren tsaki. “Mtsw!”

Shi dai bai sake tamka ta a zancen ba sai dariya da ya yi, suna tafe suna taɓa hira jefi-jefi.

 Lokaci bayan lokaci ta kan fashe da dariya domin duk abin da ta gani ko wanda ta gani a hanyar ya ba ta dariya sai ta yi, wasu kuma ta tsokane su haka har suka isa. Ɗan nesa da ƙofar gidan ta sa ya sauke ta, tana waigawa gefenta ta ga mai rake a cikin layin, ta matsa kusa da hanzari ta wafto biyu tana nuna masa Abdul da yatsa sannan ta ce “Ya biya ka.” 

Abdul tana shirin buga abin hawan nasa kenan ya ji sallamar mai rake yana tambayarsa kuɗi. Daga can ɗan nesan da ta fara tafiya ta juyo tana faɗar “Abdul ɗinmu ka bi ya mini don Allah ka ji? Ai na san kai ba matsiyaci ba ne…”

Girgiza kai kawai ya yi yana dariya a ransa ya yi mata fatan shiriya ya ciro kuɗin ya biya ya ƙara gaba.

Tana isa ta shiga gidan da sallamarta mai cike da murna, a tsakar gidan ta tarar da mahaifiyarta tana iza wutar itace da ke cikin murhun da tukunya take ajiye a kai. Sai dai tun daga mugun kallon da maman ta tarbe ta da shi ta fahimci cewa da wata a ƙasa sai fatan ba rabon shan duka ba ne ya sa ta wanko ƙafa ta zo.

Jiki a sanyaye ta isa kusa da maman tana furta “ina wuni mam…”

Kafin ta rufe baki maman ta damƙo kwalarta ta riƙe da kyau tare da janyo ta sosai kusa da ita.

Tofah! Me ke shirin faruwa da Halisa? A kan me mama take shirin hukuntata?

Surayyah fa za ta dace a wannan karon ko kuwa kaɗɗara za ta ci gaba da ɗawainiya da ita?

Ku ci gaba da biyo alqalamin Ummu Intisar don samun amsoshinku.

Ummu Intisar ce 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here