Home Siyasa 2027: Ƙungiyar Izala ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu

2027: Ƙungiyar Izala ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu

16
0

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis-Sunnah (JIBWIS), ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta bayyana goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran Sanata Abdulaziz Yari Abubakar Almansoor Gusau ya fitar ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026.

Sanarwar ta ce tawagar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC, ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ta gana da malaman JIBWIS domin neman goyon bayansu ga takarar Shugaba Tinubu.

Ta ce Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana matsayin ƙungiyar ne yayin ganawarsa da Darakta-Janar na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC, Sanata Yari, tare da tawagarsa.

A yayin ganawar, shugabannin JIBWIS sun buƙaci gwamnati ta ƙara ɗaukar matakan kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar ƙasar.

Sun kuma gabatar da wasu buƙatu da suka shafi jin daɗin al’umma da inganta rayuwar jama’a.

A nasa ɓangaren, Sanata Yari ya nemi addu’a da goyon bayan malaman ƙungiyar, tare da yin kira da a ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa da tattaunawa da jama’a gabanin babban zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here