Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Mai Dauko wa Gwamnan Kano Rahoto a Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Pharm. Ibrahim Jinjiri ya fitar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya ƙaddamar da rabon kayan domin ƙarfafa ayyukan cibiyoyin lafiya da inganta kula da marasa lafiya.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa za a raba kayan ga cibiyoyin lafiya daban-daban a jihar.





