Home Labarai Alƙalin kotu ya tsallaka ta tagar kotu lokacin da barayin daji suka...

Alƙalin kotu ya tsallaka ta tagar kotu lokacin da barayin daji suka yi yunkuri sace shi a jihar Katsina

18
0

Alkalin kotun Shari’a, Mohammed Muktar, ya tsallake rijiya da baya a ranar Laraba bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka mamaye harabar kotu a kauyen Gwarjo da ke karamar hukumar Matazu a jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne da misalin tsakar rana, inda rahotannin da jaridar Daily Trust ta wallafa suka ce maharan dauke da makamai sun kutsa cikin harabar kotun, suka rika harbe-harbe domin tsoratarwa, sannan suka nemi a nuna musu inda alkalin yake. Ana kyautata zaton manufarsu ita ce kashe shi ko kuma yin garkuwa da shi.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar cewa Mohammed Muktar ya hango maharan tun daga nesa, lamarin da ya ba shi damar tserewa ta taga cikin gaggawa, ‘yan dakiku kafin su isa cikin dakin shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here