Home Labarai Jami’ar Sokoto Za ta Yaye Ɗalibbai 6000 a bukinta karo na 8

Jami’ar Sokoto Za ta Yaye Ɗalibbai 6000 a bukinta karo na 8

3
0

Jami’ar Jihar Sokoto (Sokoto State University) ta sanar da cewa za ta yaye dalibai kimanin 6,000 a bikin yaye dalibai na takwas da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Bello Yarima, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron manema labarai da aka gudanar kafin bikin yaye daliban a birnin Sokoto.

Ya ce daliban da za a yaye sun fito ne daga sassa biyar na jami’ar, yayin da kuma za a karrama wasu fitattun mutane da lambar girmamawa ta digirin digirgir saboda gudummawar da suka bayar wajen bunkasa ilimi da ci gaban tattalin arziki a jihohin Sokoto, Zamfara, Kebbi da sauran sassan Najeriya.

Farfesa Yarima ya yabawa Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, wanda shi ne Bako na Musamman (Visitor) na jami’ar, bisa irin goyon bayan da yake bai wa jami’ar ta fuskar kuɗi da kuma ƙarfafawa.

A cewarsa, da aka gabatar wa gwamnan kasafin kuɗin bikin yaye daliban, nan take ya ƙara miliyoyin naira domin tabbatar da an gudanar da bikin cikin nasara.

Haka kuma ya yabawa wanda ya assasa jami’ar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, bisa ci gaba da bayar da gudummawa wajen ci gaban jami’ar, musamman aikin faɗaɗa ɗakin karatu na jami’ar da yake aiwatarwa ta hanyar aikin mazabarsa, wanda ya ce an kusa kammala shi.

Mataimakin Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa burinsa shi ne ganin jami’ar ta zama cibiyar koyar da sana’o’i da ƙirƙirar ayyukan yi cikin shekaru goma masu zuwa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta bai wa jami’ar umarni na samar da ɗaliban da za su kasance masu ƙirƙirar ayyukan yi, ba masu neman aiki kawai ba.

A ƙarshe, Farfesa Yarima ya jinjinawa mahukunta da ma’aikatan jami’ar bisa jajircewa da sadaukarwar da suka nuna, yana mai cewa haɗin kansu ne ya haifar da nasarorin da jami’ar ke samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here