A ranar Assabar ‘yan bindiga sun kai hari a garin Tsamiya cikin ƙaramar hukumar Bagudo a jihar Kebbi in da suka ƙone shingen bincike na rundunar tsaro ta civil difens(NSCDC), da gidan Karuwai da gidan wani Sule Mai Goge. Sun kuma yi garkuwa da Alhaji Yusuf Bazamfare.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kebbi SP Bashir Usman ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce rundunar ‘yan sanda ta tura jami’anta a garin na Tsamiya bayan da ɓatagarin suka kai harin a ranar Assabar.
Ya ce bayan da kwamishinan ‘yan sanda ya samu rahoto kai tsaye ya ba da umarnin a ƙara tura jami’an tsaro domin su tabbatar da kare rayuwa da dukiya.
“An soma binciken kan faruwar lamarin, sannan ana kan ƙoƙarin a kuɓutar da wanda aka yi garkuwa da shi, ba a tsaya ba don gano in da mutanen suka ɓoye.”
Ya ce rundunar ta ba da tabbaci ga mutanen Tsamiya da kewayensu jami’an tsaro ba za su tsaya ba har zaman lafiya ya dawo, ya nemi mutane su natsu tare da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a yankunan su.





