Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Mukaddashin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto, Imam Sirajo Abubakar ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa hukumar na neman mutanen biyu, inda ta ce jami’anta sun bazu zuwa wurare daban-daban domin gano inda suke.
A watan Fabrairun 2025 dai, ƴan uwan Y. America sun taɓa yi masa ladabi tare da neman ɗaukin hukumar Hisbah ta Kano.
Hisbah ta Kano ta yabawa ƴan uwan nasa kan ƙoƙarin da suka yi a kansa, sai dai daga baya ya sake ɓallewa.
Yanzu haka dai Y. America na rayuwa a Abuja zuwa Legas inda a kullum ya ke rungume-rungume da ƴan mata yana wallafawa a TikTok.






