A cigaba da shirye-shiryen Manyan Zabukan shekarar dubu biyu da Ashirin da da Bakwai a kasar nan, Jam’iyyar APC Mai Mulki a Nijeriya ta fitar da tsarin Jadawalin Zabukan fidda Gwani ‘Yan Takara daban-daban.
A kan haka ne, Maigirma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Sakkwato Alh. Haruna Sarkin Gobir Adiya yake sanar da dukkan magoya bayan Jam’iyyar a matakin Jiha dana kananan Hukumomi 23 dake Jihar sokoto cewa, Jadawalin Zabukan fidda Gwani za su kasance kamar haka;
A Ranar Jumu’a ta 15/5/2026 za a soma da Zabukan ‘Yan Majalisar Wakilai ta tarayya su 11 na Jihar sokoto Kamar haka; Mazabar Binji da Silame a sakatariyar Jam’iyyar dake Binji, Sai Mazabar Bodinga/Dange Shuni/Tureta a sakatariyar Jam’iyyar dake Bodinga.
Haka Kuma, Mazabar Goronyo da Gada, za a yi zaben a Makarantar GSS dake kan titin Illela a Karamar Hukumar Mulkin Gada, Sai Mazabar Gwadabawa/Illela, za a yi zaben a Makarantar sakandaren Gwamnati ta kimiyya dake Garin Gwadabawa, haka zalika a Mazabar Wurno da Rabah, za a gudanar da zaben a Makarantar furamare ta Marigayi Mu’azu dake Wurno. A Mazabar Kware da Wamakko kuwa za a gudanar da zaben a sakatariyar Karamar Hukumar dake Kware.
A Mazabar Isa/Sabon Birni, za a gudanar da zaben a filin wasa dake Karamar Hukumar Mulkin Isa, Sai Kuma Mazabar Tangaza da Gudu, zaben zai gudana a sakatariyar Jam’iyyar dake Gidan Madi na Karamar Hukumar Mulkin Tanzaga.
Sai Mazabar Sokoto ta Kudu da ta Arewa, za a gudanar da zaben a sakatariyar Jam’iyyar dake kan titin Sarkin Musulmi Abubakar Unguwar Diplomat, ya yin da za a fitar da Gwani a Mazabar Kebbe/Tambuwal a sakatariyar Karamar Hukumar dake Tambuwal,Sai Mazabar Yabo/Shagari za a yi zaben a sakatariyar Jam’iyyar dake Yabo.
Sai Kuma a Ranar Litinin 18/5/26 za a yi zaben fidda Gwani na Yan Takarar Sanatoci kamar haka.
Gundumar sokoto ta Arewa, za a yi zaben a sakatariyar Jam’iyyar dake kan titin Sarkin Musulmi Abubakar Unguwar Diplomat Sokoto. Sai Gundumar sokoto ta Kudu, za a yi zaben a sakatariyar yanki dake Bodinga haka zalika a Gundumar sokoto ta Gabas zaben zai gudana a sakatariyar yanki dake Garin Gwadabawa.
A Ranar Larba ta 20/5/2026, za a gudanar zaben fidda Gwanin na Yan Majalisar Dokoki na Jihar sokoto su Talatin a wurare daban-daban Kamar haka;
Mazabar Binji, sakatariyar Jam’iyyar dake Binji, Mazabar Bodinga ta daya a sakatariyar Jam’iyyar dake Bodinga, Mazabar Bodinga ta biyu a Makarantar furamare ta Danchadi, Mazabar Dange Shuni a sakatariyar Jam’iyyar dake Dange Shuni, a Mazabar Gada ta Yamma a Makarantar JSS Gada, a Mazabar Gada ta Gabas a Makarantar JSS dake Kadadi Sai Mazabar Goronyo a Makarantar furamare ta Goronyo.
Bugu da Kari a Mazabar Gudu za a gudanar da zaben a Makarantar GSS Gudu, Sai Mazabar Gwadabawa ta kudu za a hadu a ofishin yanki na Gwadabawa Sai Gwadabawa ta Arewa za a hadu a Makarantar furamare ta Tambagarka, da Kuma Mazabar Illela inda za a hadu a sakatariyar Jam’iyyar dake kan titin Araba. A Mazabar Isa za a gudanar da zaben a filin wasa dake Karamar Hukumar Mulkin Isa, Sai Mazabar Kebbe zaben zai gudana a sakatariyar Jam’iyyar inda Mazabar Rabah za ta yi nata zaben sakatariyar Karamar Hukumar.
Mazabar Sabon Birni ta Arewa kuwa, za su yi zaben a sakatariyar Karamar Hukumar, inda Sabon Birni ta Kudu za a yi zaben a Makarantar sakandaren Gatawa dake Karamar Hukumar.
A Mazabar Shagari, za a yi zaben a sakatariyar Jam’iyyar Sai Mazabar Sokoto ta Arewa ta daya zaben zai gudana a Makarantar furamare ta Waziri Sai sokoto ta Arewa ta biyu za a yi zaben a sakatariyar Jam’iyyar ta Jiha.
Mazabar Sokoto ta Kudu ta daya zaben zai gudana a Makarantar furamare ta Ibrahim Gusau Sai sokoto ta Kudu ta biyu za a yi zaben a Makarantar furamare ta Muhammad Bankanu dake kan titin Koko sokoto.
A Mazabar Silame za a yi zaben a sakatariyar Karamar Hukumar, zai Tambuwal ta Yamma zaben zai gudana a sakatariyar Karamar Hukumar, Sai Tambuwal ta Gabas za a yi zaben a Makarantar furamare ta Garin Dogon Daji, Mazabar Tangaza, zaben zai gudana a sakatariyar Jam’iyyar dake Gidan Madi.
A Mazabar Tureta za a yi zaben a sakatariyar Jam’iyyar dake Tureta Gari, ya yin da Mazabar Wamakko zaben zai gudana a Makarantar furamare dake Wamakko.
A Mazabar Wurno, za a yi zaben a Makarantar furamare ta Marigayi Mu’azu, Mazabar Yabo, za a yi zaben a masauki baki na Gwannati dake Yabo Sai Mazabar Kware zaben zai gudana a sakatariyar Jam’iyyar APC dake Kware.
Da fatan Allah ya bada ikon zuwa, a yi lafiya a Kare lafiya, allahumma Amin.
Sanarwa daga Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar sokoto Alh. Haruna Sarkin Gobir Adiya.





