Home Finafinnai Rikici a Kannywood: Dalilin Dawayya Na Maka Rashida Mai Sa’a Kotu

Rikici a Kannywood: Dalilin Dawayya Na Maka Rashida Mai Sa’a Kotu

16
0

Kotun majistiri mai lamba 9 da ke Nomansland a Kano, ƙarƙashin mai shariʼa Halima Wali ta hana jarumar Kannywood Rashida Adamu Mai Saʼa yin posting a social media har sai an gama shariʼar da Ruƙayya Dawayya ta yi ƙararta kan zargin ɓata suna.

Dawayya tana ƙarar Mai Saʼa ne bisa zargin ɓata mata suna da cin mutunci da hana zaman lafiya.

An zarge ta da cewa a ranar 15 ga Janairun 2026 ta yi wani bidiyo wanda ta yaɗa a kafafen sada zumunta, inda a ciki ta ci mutuncin Dawayya da cewai wai ta je wajen wani ɗan siyasa ta yi abin da bai dace ba a jihar Gombe.

Bayan karanta mata zargin ɓata suna, da cin mutunci da hana zaman lafiya duka ta musanta.

Lauyoyinta sun nemi a sanya ta a beli, inda kotun ta amince bisa sharaɗin za ta kawo ɗan majalisar jiha mai ci, da kuma ɗan uwanta wanda ya ke da gida ko fili da bai gaza Naira Miliyan 300 ba a Kano.

Sannan kotun ta yi umarnin a karɓe wayoyinta, kuma kar ta kuma wallafa wani abu a shafukanta na kafafen sadarwa har sai an kammala shariʼar.

Kotun ta sanya ranar 20 ga watan Mayun da muke ciki domin ci gaba da shariʼar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here