Kotun kolin Najeriya ya tabbatar da Dauda Lawal a matsayin sahihin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, rahoton Channels Tv.
Tabbatarwar na zuwa ne kwanaki hudu gabanin zaben gwamna da za a yi a Najeriya a ranar 11 ga watan Maris kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta tsara.
Kotun daukaka kara mai zamansa a jihar Sokoto a ranar 6 ga watan Janairu ya yi watsi da hukuncin kotun tarayya da ya kori Dauda a matsayin dan takarar da zaben fidda gwanin PDP a Zamfara ya samar.
An kalubalanci zaben fidda gwanin ne a kotun tarayya da ke zama a Gusau, babban birnin Zamfara, inda alkali ya umarci a sake yin sabon zaben na fidda gwani.





