Home Uncategorized Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi Ta Rasu 

Mahaifiyar Sheikh Ahmad Gumi Ta Rasu 

8
0

Mahaifiyar fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ta riga mu gidan gaskiya. 

Bayanai sun nuna cewa mahaifiyar Malamin ta rasu ne a wani Asibiti dake birnin tarayya Abuja da yammacin yau Lahadi, 5 ga watan Maris, 2023. 
Shehin Malamin ya tabbtar da rasuwar mahaifiyarsa a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook. Ya ce ta rasu da misalin ƙarfe 5:30 na yamma. 
“Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, da zuciya mai rauni nake sanar da rasuwar mahaifiyata, yau da misalin karfe 5:30 na yamma. 
Dan Allah ku tama ni roka mata gafara da rahamar Allah.” 
“Kalamai na karshe da ta faɗa mun mako uku da suka gabata; In Sha Allah, Allah zai sanya ta da ‘ya’yanta da jikokinta wuri ɗaya a cikin gidan Aljannah.” 
“Waɗan nan kalmomi suna kwantar mun da hankali, Allah ya tabbatar da rahamarsa a gareta, Amin.” 
Wata sanarwa mai biye wa wannan a shafin Malamin na Facebook ta ce za’a yi jana’iza gobe Litinin 6 ga watan Maris, 2023 a ƙofar gidan Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. 
Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa za’a gabatar da Jana’iza da Azahar misalin karfe 1:00 a gidansu da ke Anguwar Sarki, GRA bayan Lugard Hall cikin garin Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here