Home Manyan Labaru Jirgin Sojoji ya kashe mutane sama da 200 a Yobe

Jirgin Sojoji ya kashe mutane sama da 200 a Yobe

7
0

Ƙungiyoyin farar hula da masana harkar tsaro a Nijeriya sun nuna damuwarsu kan jirgin sojojin sama da ya yi ɓarin wuta a kasuwar sati-sati da ke kan iyakar jihar Borno da Yobe in da suka kashe sama da mutum 200 ‘yan kasuwa bayan wasu da suka jikkata suna asibiti don karbar magani.

Lamarin da ya faru a ranar Assabar da marece a kasuwar Jilli dake tsakanin Gubio da Gaidam ƙananan hukumomin Borno da Yobe.

A bayanin da sojojin suka fitar ta hannun mai Magana da yawun rundunar Haɗin kai Sani Uba ya ce ɓatagari ne aka jikkata a harin.

Ya ce an ɓarnata ababen hawa yayin da waɗanda suka tsira sun gudu warare daban daban.

Wani wanda ya ga harin da idonsa Umar Bomai ya faɗawa Daily Trust kusan mutum 200 aka kashe a harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here